
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya isa birnin Kebbi babban birnin jihar Kebbi inda zai gana da iyayen daliban Makarantar Sakandaren Yan Mata dake Maga da wasu yan bindiga su ka yi garkuwa da su.
Shettima ya isa birnin da tsakar ranar Laraba bisa umarnin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Stanley Nkwocha mai magana da yawun Shettima ya ce mataimakin shugaban kasar ya samu tarba daga Nasiru Idris gwamnan jihar, sarakunan gargajiya da kuma shugabannin hukumomin tsaro.
Tinubu ya umarci Shettima da ya kai ziyara jihar domin ya tabbatarwa da iyaye da wakilan É—aliban da aka sace cewa gwamnatin tarayya na yin duk mai yiyuwa wajen ganin an kubutar da su daga hannun waÉ—anda suka sace su.
A yayin ziyarar mataimakin shugaban kasar na tare da Bernard Doro ministan ma’aikatar jin kai da yaki da talauci, ministar ma’aikatar mata, Imaan Abba Ibrahim da kuma Zubaida Umar shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA.

