Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya dawo gida Najeriya bayan da ya halarci Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 da ya gudana a hedkwatar majalisar dake birnin New York a ƙasar Amurika.
Shettima ya wakilci shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu a wajen taron inda ya gabatar da jawabin Najeriya a wurin babban taron.
Da yake jawabi a wurin taron Tinubu ya buƙaci a yafewa Najeriya basukan da ake bin ta.
A wata sanarwa ranar Lahadi, Stanley Nkwocha mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar ya ce Shettima ya halarci wasu taruka da dama a wurin taron.
Nkwocha ya ce bayan dawowarsa Shettima zai haɗu da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu inda za su halarci wasu taruka da suka shafi murnar bikin ranar samun ƴan cinkan Najeriya.