HomeHausaSheikh Jarrah: Me ya sa ake ƙwace wa Falasɗinawa gidajensu a birnin...

Sheikh Jarrah: Me ya sa ake ƙwace wa Falasɗinawa gidajensu a birnin Kudus?

Published on

spot_img
  • Daga Reality Check team
  • BBC News
Palestinian man gestures to Israeli police in Jerusalem (10/05/21)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
Tashin hankali ya ƙaru a farkon watan nan a birnin Ƙudus

Iyalan Falasɗinawa da ke fuskantar kora daga gidajensu a wata unguwa da ke gabashin Kudus sun ce za su yi watsi da shawarar da Kotun Kolin Isra’ila ta bayar cewa su mika gidajensu ga Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna.

A madadin haka, su kuma Yahudawan za su ba su damar ci gaba da zama a matsayin ‘yan haya a unguwar Sheikh Jarrah. Kotun ta ce idan Falasdinawa suka amince, to za ta ba su kariyar doka domin ci gaba da zama a unguwar.

Su dai iyalan Falasdinawan sun so ne kotun ta amince da cewa gidajen nasu ne.

Batun wannan unguwa ta Sheikh Jarrah ya zama babban al’amari ga dukkan Falasdinawa, kuma shi ne abin da ya haifar da kazamin rikicin baya-bayan nan tsakain kungiyar Hamas da Isra’ila a Zirin Gaza.

Rashin tabbas kan makomar iyalai a yankin Sheikh Jarrah – da wasu ke fuskantar barazanar tilasta musu fita daga gabashin Kudus – ya haifar da gaggarumar zanga-zanga da rikici na tsawon makonni.

Me ke haifar da rikicin?

Sheikh Jarrah wani yanki ne na Falasdinawa wanda Isra’ila ta mamaye a Gabashin Kudus, kusa da tsohon birni da kuma wurin bauta.

An jima ana tafka rikici kan ainihinmallakin yankin, wanda yahuduwa ke korar Falasdinawan da ke zaune a yankin tun bayan hijira.

Wannan ɗan karamin garin a Kudus ya kasance ginshiki a rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

Isra’ila na ɗaukan yankin baki ɗaya tamkar babban birninta – batun da ƙasashen duniya da dama ba su aminta ba.

Falasdinawa na son gabashin Kudus ya kasance babban birninsu a nan gaba a fatansu na kafa ƙasar Falasdinu.

Me ke faruwa a Sheikh Jarrah?

Kungiyoyin Yahudawa sun saye yankunan a kusa da wajen ɓautarsu na Shimon Hatzadik, a Sheikh Jarrah, a 1876, kuma akwai mutanen da suka shafe tsawon shekaru suna rayuwa a yankin.

Amma bayan yakin Larabawa da Isra’ila tsakanin 1948-49, birnin Kudus, inda Larabawa da Yahudawa ke rayuwa tare, an raba shi tsakanin Isra’ila da masarautar Jordan.

Yaduwa sun ɗaiɗaita daga gabashi, sannan Falasdinawa daga yammacin rabin birnin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
An yi ta rikici a Sheikh Jarrah a watan Mayu

Sannan kuma Jordan na iko da gabashin Kudus, wanda ya kasnace wani nauyi ga Falasdinawa yan gudun hijira da suka koma yankin.

Da taimakon Majalisar Dinkin Duniya, mahukuntan Jordan sun gina gidaje 28 ga wasu daga cikin masu hijirar, a yankin Sheikh Jarrah wanda a baya ke hannun mahukunta Yaduwa amma Jordan ta ƙwace.

Waɗanan iyalai an alkawarta musu – amma basu taba karba ba – yankin a shari’an ce.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,
Isra’ila ta mamaye Gabashin Ƙudus

Amma bayan yakin 1967, Isra’ila ta mamaye gabashin Kudus da kirkiro nata dokokin – waɗanda MDD ta ce bai halasta ba.

A 1970, an bijiro da wata doka domin bibiyar rigingimu da ake yi kan ainihin wanda ya mallaki yankuna irinsu Sheikh Jarrah.

Falasdinawa, ko da yake, su ma ba su da ƴancin dawo da ƙadarorinsu da suka rasa a Yammacin Kudus, da sauran wuraren a Isra’ila, wanda a karkashin dokokin 1950 aka sanar a matsayin wanda aka yasar kuma ya koma karkashin Isra’ila, sai dai suna iya neman diyya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
A watan Yuni ƴan sanda suka tuhumi wata mai fafutuka Muna el-Kurd, mazauniyar Sheikh Jarrah

Wasu Falasdinawa na samun gurbin kariya, wanda ke kunshe a yarjejeniyar 1982, wanda iyalai 17 suka ci gajiya a Sheikh Jarrah.

Sai dai wannan ya tabbatar da yarjejeniyar ƙadarori ta ƙarni na 19 wanda yahudawa suka gabatar wanda kuma ke nufin iyalai za su biya kuɗin haya ga sabbin mutane da suka mallaki kadarorin, sannan sai sun nemi izini kafin fadada gidajensu.

Iyalai daga baya sun yi watsi da yarjejeniyar.

Kuma akwai rashin tabbas kan ko Falasdinawa suna sane da yarjejeniyar da suka amince.

A shekarun 1990, iyalai sun daina biyan haya kuma yahudawa sun shigar da kara a kansu.

A 2020, kotu a Kudus ta samu Nahalat Shimon da laifi da kuma bada umarni su fice tare da sauran iyalai, matakin da ya shafi iyalai da dama.

Kotun koli ta yi kokarin shiga tsakanin sansanonin biyu – kuma daftarin ya kunshi batun biyan haya ga iyalai – amma tattaunawar ta gaza.

Mazauna yanki na so a tabbatar da kadarorin a matsayin nasu – amma iyalai sunƙi aminta.

Sannan kotun koli na nazarin kan hukuncin aminta ko kin amincewa da daukaka kara da lauyoyin wakilan iyalan Falasdinawa suka shigar a Sheikh Jarrah.

Sun shafe tsawon shekaru 70 a wadanan gidaje.

Yanzu haka suna fuskantar barazanar rasa muhallansu a karo na biyu a tarihi.

Asalin hoton, EPA

MDD ta ce dokokin da ke fayyace wanda ke da iko kadarori a Kudus ” akwai son kai a ciki domin akwai banbance-banbance tsakanin ɗan kasa da aihinin mallakin wuri”.

Amma gwamnatin Isra’ila ta ce tana da yancin gini a birnin da ta dauka tamkar babban birninta – kuma batu kora abu ne da ya kunshi mallakan gidaje da masu hakki da yan haya za su warware.

Misalin da ke a bayyana shi ne na gasar da ake yi kan hakkin mallaka.

Otel din Shepherd, a Sheikh Jarrah, misali an bayyana shi a matsayin wanda babu mallaki, karkashin dokokin Isra’ila kuma matsayin ya kai har zuwa ga wani attajirin Amurka ya saye shi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
Falasdinawa na zargin Isra’ilawa da kokarin kawar da su daga birnin

Akwai mazauna kusan 3,000 wanda suka kasance Falasdinawa a gabashin Kudus – kusan dukkaninsu a ciki da kewayen tsohon birane irinsu Sheikh Jarrah, a cewar wata kungiyar Isra’ila mai zaman kanta, peace now.

Kuma tun farkon shekara ta 2020, wata kotu ta umarci a fitar da iyalai 36 daga Batan Al-Hawa da Sheikh Jarrah, wanda yanzu haka aka daukaka kara kan hukuncin.

A kewayen birnin, MDD ta kiyasta cewa Falasdinawa 70 na cikin barazana rasa muhallansu sakamakon shari’ar da ke gaban kotun Isra’ila.

Tsarin dokokin kuma ya kasance mai wahala ga Falasdinawa na iya fadada gidajensu.

Tsakanin 1991 zuwa 2018, gidaje 9,536 aka amince Falasdinawa su gina a gabashin Kudus, wanda bai kai 21,834 da aka yarje kan Isra’ila ba, a cewar kungiyar Peace now.

Kuma saboda irin waɗanan tasgaron, anyi gine-gine da dama da suka saɓa dokoki, abin da ya kai ga mahukunta Isra’ila na ruguza su.

(BBCHausa)

Latest articles

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin...

More like this

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...