Shehun Borno, Alhaji (Dr) Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, ya yi kira da a dage da addu’a domin Allah ya kawo dauki kan karancin ruwan sama a wasu sassan jihar Borno.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Zanna Laisu Kazalma, Sakataren Majalisar Masarautar Borno, Shehun Borno ya yi kira ga dukkan Limamai da su ba da addu’o’i na musamman daga ranar Juma’a, 21 ga Yuli, 2023 don neman taimakon Allah Ta’ala.
Shehu ya umurci dukkan hakimai da ƙauye a fadin jihar da su hada kan al’ummar Musulmi a yankunansu domin kai dauki ga mabuƙata, marayu da nakasassu.
Ya kuma shawarci iyaye da su rika yi wa ’yan uwa nasiha kan su guji dabi’u na fasikanci, munanan dabi’u, da shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Sannan ya bukaci daukacin ‘yan kasuwa da su ji tsoron Allah wajen gudanar da sana’arsu ta halal.