
Stan Lee ne ya rubuta labarin fim din Spiderman da The incredible hulk da kuma Captain America
Stan Lee mai shekara 95, a lokacin da ya ke kan ganiyar aikinsa, shi ya kirkire labarin fina-finan nan na ban dariya, da nuna bajinta wato Spiderman da The incredible hulk da kuma Captain America.
Gidajen sinima a fadin duniya sun yi cinikin sama da dala biliyan 20 ta hanyar wadanan fina-finai.
Shugaban kamfanin shirye fina-finai na Walt Disney, wanda yanzu haka ya mallaki Marvel ya ce Stan Lee wani mutum ne na daban, kamar yadda jaruman fina-finan da ya kirkira suke.
Ya kuma ce Stan Lee dan baiwa ne da ya ke da basirar nishadantarwa da kuma karfafa wa wasu kallo da bibiyar fina-finai ko ayukansa gwiwa.