Duk mutumin da yake karatu a manyan makarantun Najeriya — kama daga jami’o’i har zuwa kwalejojin horas da malamai da kwalejojin fasaha — ya san irin hali tare da mummunan tarkon malamai maza da ɗalibai mata suke faɗawa. Abin ya munana sosai har ya kai matakin da idan malami ya nemi yin lalata da ɗaliba sannan ta ƙi ba shi haɗin kai, akwai yiwuwar ya yi ta kayar da ita a darasin da yake koyarwa. Amma da zarar ta miƙa wuya, tana iya fin kowa samun maki ko da kuwa ba ita ta fi kowa ƙoƙari a ajinsu ba. Abubuwa irin waɗannan sun sha faruwa a jami’o’in Najeriya kamar yadda zan kawo a nan gaba.
A watan Afrilun 2018, jaridar Premium Times, wata babbar kafar yaɗa labarai a Najeriya, ta rawaito yadda aka zargi wani Farfesa Richard Akindele na Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife da neman yin lalata da wata ɗaliba. Shi wannan farfesan ka’ida ya gindaya wa ɗalibar tasa mai suna Monica cewa sai ta amince ya kwanta da ita sau biyar kafin ya bar ta ta ci jarabawar kwas ɗin da yake koyarwa. Ashe lokacin da yake gindaya mata waɗannan sharuddan, tana ta naɗar muryarsa a waya. Daga baya sai ta tona masa asiri.
Baya ga wannan, a watan Afrilun 2019, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, wani shugaban tsangaya a Jami’ar Abuja shi ma ya nemi yin lalata da ɗalibarsa kafin ya bar ta ta ci jarabawar kwas ɗin da yake koyarwa. Ita kuwa, wataƙila saboda ba ta son zubar da mutuncinta, sai ta je ta kai ƙara wa jami’an tsaron jami’ar da kuma hukumar ‘yan sanda don a kiyaye mata mutuncinta. Daga nan, sai aka yi masa tarko bayan ya kama musu otel don su yi lalatar. Kwatsam kawai sai jami’an suka zo suka iske shi.
Ga shi a kwanakin nan ma irin haka ya faru — har ila yau kamar yadda Daily Trust ɗin ta sake bincikowa, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda har wani farfesa mai ɗauke da cutar ƙanjamau ya lalata wata daliba mai ƙarancin shekaru. Ga kuma wani labarin da BBC Hausa ta rawaito na yadda ake musguna wa ɗalibai mata idan sun ƙi mika kansu ga lalatattun malamai. Wasu kam ma har matan aure ba su bari ba. Misali, kwanan nan wata matar aure ta mutu sanadiyar juna biyu da ta samu bayan ta kwanta da malaminta (labarin ya bazu a kafofin sada zumunta sosai). Irin waɗannan labaran idan za a ci gaba da kawo su, za a iya kawo sama da dubu don bala’in ya zama ruwan dare gama duniya.
Maganar gaskiya ita ce, lokaci ya yi da duk za mu tashi tsaye wajen yaƙar wannan masifa domin idan bai samu ‘yarka ba, zai samu wata ‘yar uwarka ko wata da kake da alaƙa da ita. Abin kunya ne matuƙa. Yanzu su masu irin wannan halin ba sa tunanin suna da ‘ya’ya ko ‘yan uwa mata a wasu wuraren ne? Ba za su tausaya wa al’umma ba?!
Laccarori masu irin wannan halin ya kamata su ji tsoron Allah su daina. Aiki suke yi ana biyansu. To mene ne kuma mutum zai ce sai ɗalibarsa ta ba shi wata dama kafin ta ci jarabawa duk ƙoƙarinata? Wannan ba daidai ba ne.
Duk da cewa sau tari za ka samu wasu ɗaliban su ke miƙa kansu da kansu ba tare da malami ya buƙaci su yi hakan ba, amma bai dace a ce kuma an samu irin wannan mummunar alaƙa tsakaninsu ba.
Iyaye, ku saka ido a kan ‘ya’yanku. Kar ku tura ‘yarku makaranta sannan kawai ku sake jiki ku zuba mata ido. Dole ne ku riga shiga al’amuranta; ku riƙa son jin matsalolin da take fuskanta domin neman mafita. Babu iyayen da za su so ‘yarsu ta lalace domin kwata-kwata ba daɗi!
Daga ƙarshe, zan yi kira ga shugabannin jami’a da na kwaleji, da shugabannin tsangaya da shashe da kuma su laccarorin kansu cewa ya kamata su san yara da ake kawo masu a matsayin ɗalibai ba komai ba ne illa “amana” da iyaye suke danƙa masu. Kuma ana kai yara makaranta ne don su sami ilimi da tarbiyya. Sannan, ya kamata a samar da ƙwararan dokoki masu matuƙar tsauri da za su kiyaye mutuncin ‘ya mace da malamai masu mutunci a jami’o’i da kwalejoji domin a sami ingantacciyar al’umma — ba lalatacciya ba.
Muhammadu Sabiu ne ya rubuto wannan maƙala daga Bauchi. Za a iya samunsa ta 09078713542.