Sauyin Sheka Ya Sa An Kori Dan Majalisar Jiha a Neja

[ad_1]

Majalisar dokokin jihar Neja ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda dan majalisar ya canza sheka daga APC mai Mulki zuwa Jam’iyyar Adawa ta PDP kuma ta ayyana kujerarsa a matsayin wadda babu kowa akanta.

Shugaban majalisar Dokokin jihar Neja Hon. Ahmad Marafa Guni, a wata hira ta waya da wakilin sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari, ya ce uwar jam’iyyarsu ta APC ce ta kawo korafi akan dan Majalisar da ya canza sheka shi ya sa suka dauki matakin.

To amma dan majalisar da aka kora Hon. Danladi Iya yace zai je kotu domin kalubalantar wannan matakin. Hakazalika shima shugaban Marasa rinjaye a majalisar, Hon. Bello Agwara yace Majalisar tayi saurin daukar Matakin korar, ya kara da cewa kamata yayi abi doka.

Kokarin jin ta bakin shugabannin Jam’iyyar ta APC a jihar Neja ya ci tura, sai dai mai taimakawa gwamnan jihar Neja akan harkokin Majalisar Wanda kuma jigo ne a jam’iyyar APC, Hon. Abdulhamed El’wazir yace majalisar tayi aikinta ne.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari

[ad_2]

More News

Ƴanbindiga sun kashe mataimakin shugaban jami’ar UDUS

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe mataimakin shugaban jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Yusuf Sa’idu.Jami’ar wadda ta bayyana rasuwar...

NDLEA ta kama tan 761,000 na miyagun kwayoyi cikin shekaru 3

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Buba Marwa, ya ce hukumar ta kama tan 761,000 na haramtattun kwayoyi...

An saka jirage uku na  shugaban ƙasa a kasuwa

Gwamnatin Najeriya ta saka jiragen shugaban ƙasa guda uku a kasuwa a wani yunkuri da mahukunta suka bayyana da cewa zai rage yawan kuɗaɗen...

Ƴan bindiga sun kashe mai POS a Ekiti

Wasu ƴan bindiga sun kashe wani mai sana'ar POS a garin Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti. Mai sana'ar ta POS dake da suna Alfa Taofeek...