Sauyin dokar zaɓen Najeriya na tayar da ƙura

Shugaban majalisar dattawan Najeriya

Asalin hoton, @DRAHMADLAWAN

Batun sauya dokar zaɓe da gyare-gyaren da majalisa dattawan Najeriya ta yi na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar.

Bayan jan kafa na wani tsawon lokaci da matsin lamba, majalisar dattawan Najeriya ta ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC zaɓin amfani da intanet domin tura sakamakon zaɓe.

Sai dai majalisar dattawan ta ce ba ta yarda da tsarin a aika alƙalumman sakamakon zabe ta intanet ba kaitsaye, sai dai ainahin hoton takardar sakamakon zaben da wakilai suka sanya wa hannu.

A zaman da ta yi na ranar Talata, majalisar dattawan ta ce INEC za ta iya amfani da na’ura ta aika sakamakon zaɓe a lokacin da ya dace idan har hukumar kula da harakokin sadarwa ta Najeriya NCC ta amince.

Majalisar ta kuma kaɗa kuri’ar amincewa da tsarin gudanar da zaɓen fidda ƴan takara na jam’iyyu ta hanyar zaɓe kai tsaye tare da sa idon hukumar INEC.

Majalisar a baya ta ƙi yarda hukumar zaɓen ƙasar ta aika da sakamakon zaɓe ta na’ura, yanzu ta yi gyare-gyaren da a yanzu INEC tana da wuƙa da nama a hannunta na zaɓi tsarin da za ta bi wurin aikewa da sakamakon.

A hirarsa da BBC shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriyar Sanata Yahaya Abdullahi, ya bayyana cewa sun ɗauki wannan mataki ne saɓanin na da wanda suka yi la’akari da cewa akwai wurare da yankuna na kan iyaka a kusan ko’ina a faɗin ƙasar inda intanet ba ta kai ba, waɗanda kuma a sakamakon hakan za a iya yin maguɗin ƙuri’u.

Asalin hoton, @DRAHMADLAWAN

Sanatan ya ce bayan wannan ma kuma akwai yuwuwar ƴan ɓata-gari su iya yin kutse su sauya sakamakon zabe.

A bisa la’akari da waɗannan matsaloli ne majalisar a yanzu ta yarda cewa hukumar zaɓe za ta iya amfani da hanyoyi na intanet kamar manhajar WhatsApp da makamantansu ta aika da hoton takardar sakamakon wadda wakilai da sauran masu ruwa da tsaki suka sanya wa hannu, wanda hakan abu ne mai wuya a sauya sakamakon.

Hakan na nufin a yanzu hukumar za ta iya yi wa kanta zaɓin da ta ga ya dace, wato ta aika sakon ko dai ta hanyoyin intanet ko kuma ta hanyar da aka saba bi a baya ta takarda.

Sai dai yayin da wasu ƴan ƙasar ke ganin cewa majalisar dattawan ta bayar da kai bori ya hau ne a sakamakon matsi da suka da ta sha, kan ƙin amincewar da ta nuna a baya ga tsarin aikawa da sakamakon ta intanet.

Ɗan majalisar ya ce ko alama ba haka ba ne, sun yi nazari ne kuma suka yi sauyi wanda a yanzu suka amince da wanda suka gabatar.

Wannan ana ganin ya zo daidai da bukatun yan najeriya ne musammam masu korafin cewa rashin bayar da damar ga INEC kamar kwacewa hukumar ne damar da dokokin zabe suka bata.

Masana siyasa a Najeriya kamar Malam Kabiru Sufi, na ganin dama ce yanzu ga hukumar zabe ta yi amfani da zabin guda biyu na aika a rubuce sannan kuma ta aika ta hanyar sadarwa.

Ya ce hanyoyin biyu za su hana yin maguɗi idan aka yi amfani da su. “Idan alkalumman da aka aika a hanyoyin biyu sun yi daidai zai nuna cewa ba a yi magudi ba,” in ji shi.

Yanzu abin da ya rage ga waɗannan sauye-sauye da majalisar dattawan ta Najeriya ta yi shi ne kwamitinta na daidaito mai mutane 14 zai zauna ya sake duba dokar zaɓen da kyau kafin a miƙa ta ga Shugaban ƙasar Muhammdu Buhari, wanda zai duba ya kuma sanya mata hannu.

Takaddama a kan soke tsarin zaɓen ƴan takara

Gyaran da majalisar dattawan ta yi, inda ta aiwatar da cewa daga yanzu duk wanda zai tsaya taƙara a kowa ne mataki ƴan jam’iyya ne za su zaɓe shi a fili kai tsaye maimakon tsarin da, wanda wakilai ko daliget (delegates) ke zaɓen ƴan takara, na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a ƙasar.

Majalisar dattawan a zaman na ranar Talata ta amince cewa daga yanzu duk wanda zai tsaya ko da takarar kansila ko shugaban ƙaramar hukuma ko ɗan majalisar jiha ko sanata ko gwamna ko ma shugaban ƙasa, ƴan jam’iyya masu rijista ne za su yi layi su zabe shi, domin yi wa jam’iyya takara, tsarin da ake kira ƴar-tinƙe ko ƙato bayan ƙato.

Asalin hoton, @DRAHMADLAWAN

Wasu daga cikin ƴan majalisar sun nuna cewa sun ɗauki wannan mataki ne domin magance matsalar murɗiya da danniya da kuma yadda wasu masu kuɗi ko iko ke amfani da ƙarfin mulki su murɗe zaɓe.

Sai dai kuma babbar jam’iyyar hamayya ta Najeriyar, PDP, ta soki wannan sauyi da ƴan majalisar suka yi ga dokar zaɓen ƙasar na kawo tsarin na ƴar tinƙe.

Sanata Umar Ibrahim Tsauri, sakataren jam’iyyar ta PDP a hira da BBC ya ce matakin bai dace ba, ya ce duk wanda ya yi wannan tsari ya gina wa kansa rami kuma zai fada, domin ko ba komai zai dawo da siyasar kuɗi har ma ta samu gindin zama, wadda ya ce ana ƙoƙarin kauce mata.

Ya yi bayani da cewa duk wanda zai kashe naira dubu ɗaya domin ya ci zaɓe idan za a yi zaɓe na kai tsaye ne to sai ya kashe naira dubu goma.

Sakataren na PDP ya ce kamata ya yi idan suna son a canja tsarin shi ne ya zama duk jam’iyyar da take son ta yi zaɓen kai tsaye na fitar da ƴan takara sai ta yi amma ba a sa shi a cikin dokar zaɓe ba.

Ya ce wannan bai yi daidai ba kamar an takura wa kowace jam’iyyar siyasa ne.

More News

Kar a yi saurin yanke wa gwamnatin Tinubu hukunci—in ji Yakubu Gowon

Tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon, ya yi gargadin cewa kada a yi gaggawar yanke hukunci kan ayyukan gwamnatin shugaba Bola Tinubu. Gowon ya bayyana haka...

Ƴan sanda sun kama wasu sojan gona biyu

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta ce ta kama ta ce ta kama wasu sojan gona guda biyu Jonathan Yahaya da Muhammad Umar. Benjamin Hundeyin...

Ƴan sanda sun kama wasu sojan gona biyu

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta ce ta kama ta ce ta kama wasu sojan gona guda biyu Jonathan Yahaya da Muhammad Umar. Benjamin Hundeyin...

Ƴan sanda sun kama wani dillalin miyagun ƙwayoyi a jihar Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta kama wani mai suna,Orji Isaac ɗan shekara 67 da aka samu da laifin sayar da miyagun kwayoyi a...