A yayin da ake tunanin cewa an fara samun sa’ida da kuma sauki game da satar mutane domin neman kudin fansa a wasu jihohi na arewa-maso-yammacin Najeriya, wasu na ci gaba da kokakawa kan irin matsalolin da ake samu na garkuwa da mutane.
Jama’ar da ke iyaka da jihohin Kaduna da Zamfara da kuma Neja na kukan cewa an bar irin wadannan ‘yan bindiga suna cin karensu babu babbaka a dajin da ke yankin.
Ko a yammacin Asabar sai da wasu mahara suka shiga kauyen Kurebe da ke karamar hukumar Shiroro na jihar Neja, inda suka harbi mutum biyu da yin awon-gaba da shanu masu dinbin yawa.
Sai dai wani matashi da ya samu tsira bayan ya kwashe sama da kwana arba’in a hannun masu satar mutane, wanda ya ce yanzu haka ya koma wani na daban inda yake neman aikin da zai yi saboda tashin hankalin da yankin na su ke ciki a kullu-yaumin, ya ce abin kara kamari yake yi a dajin da ke tsakanin wadannan jihohi uku.
Ganin cewa matashin ya dade hannun ‘yan bindigar kuma ya ga yadda suke cin karensu babu babbaka, ya shaida wa BBC cewa bai bayan irin abubuwan da ya gani a wannan wuri, bai yi tsammanin matakan da jami’an tsaro ke dauka a yanzu ba ko za su magance wannan lamarin.
Ya bayyana cewa har yanzu akwai wasu kauyukan da ‘yan bindigar ke masu barazana inda suke cewa sai sun bayar da kudi kafin su bar su su noma gonakinsu.
Batun garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa matsala ce da ta dade tana ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya musamman a jihohin arewa mmaso yammacin kasar.
Sai dai da alamu duk da tashi tsaye da wasu gwamnatocin jihohi suka yi domin kawo karshen lamarin, har yanzu hakarsu bata cimma ruwa ba.