Sarkin Zuru ya rasu a birnin London

Muhammad Sani Sami, Sarkin Masarautar Zuru dake jihar Kebbi ya rasu.

Sarkin ya rasu a ranar Asabar yana da shekaru 81 a wani asibiti dake birnin London.

Gwamnatin jihar Kebbi ce ta sanar da rasuwar marigayin a cikin wata sanarwa da Ahmad Idris mai magana da yawun gwamnan ya fitar a ranar Lahadi.

Idris ya rawaito kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Garba Umar Dutsinmari na cewa sarkin ya mutu a birnin London bayan gajeriyar rashin lafiya.

Umar Dutsinmari ya ce nan gaba kadan za a sanar da lokacin jana’izar marigayin.

“Gwamnatin jihar Kebbi na amfani da wannan dama wajen mika sakon ta’aziya ga iyalan marigayin, Masarautar Zuru, al’ummar Zuru da ma baki dayan al’ummar jihar Kebbi,” a cewar sanarwar.

Marigayin ya kasance gwamnan mulkin soja na jihar Bauchi daga shekarar 1984 zuwa 1985 a lokacin mulkin shugaba Muhammad Buhari.

A shekarar 1995 ne aka naÉ—a shi Sarkin Zuri.

More from this stream

Recomended