Sarkin Musulmi Ya Yi Karin Haske Kan Dalilin Su Na Matsayar Daidaita Ganin Wata

[ad_1]

Tun bayan sanarwar ganin jinjirin watan sallah babba da majalisar koli kan harkokrin addinin musulunci da kwamitin ganin wata da majalisar mai alfarma sarkin musulmi suka yi farkon wannan makon ya jawo cece kuce ciki da wajen wannan kasar.

A jiya Litinin 13/8/2018 Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi karin haske akan dalilin su na wannan matsayar. Sarkin musulmi yace ba shine kashin kanshi ya yanke wannan hukuncin ba, Manyan Malumma ne, Sarakuna da shugabannin kungiyoyin addinin musulunchi sukayi wannan matsaya bayan doguwar tattaunawar da aka dauki lokaci ana yi, daga baya aka sanar da ni matsayar da aka cimma, na amince na sanar da Shugaban na majalisar koli kan harkokin addinin musulunchi a Nijeriya ya bayyana cewa fatan su, samun hadin kan al’ummar musulmi a wannan kasar ba darewar taba. Inda yace azumin ranar Arfa, layya, sallar layya dukkan su sunna ne, amma hadin kan musulmi wajibi ne”, injishi.

Sarkin yayi bayanin cewa shekaru shida da suka gabata an yi wani taro da dukkanin shugabannin kungiyoyin addinin musulunchi a wannan kasar kuma dukkan shugabannin suna gun malummam sukayi fatawa da matsayar idan aka samu irin wannan rudanin to ayi sallah dai dai da saudiyya, domin al’ummar mu su samu damar Azummatar Ranar Arfa.

Sarkin ya ce a lokacin da ake tattaunawar sun samu kiraye kiraye daga kasashe daban daban na musulmin duniya domin su san matsayar kasar najeriya yayin da wasu kasashe kamar Maleshiya suka ce sun dauki dukkan matsayar da wannan kasar tadauka, inda wasu sukace baza bi saudiyya ba.

Zuwa yanzu dai majalisar kolin ta tabbatar da amincewar sarkin musulmi na yin sallah tare da kasar saudiyya, domin samun damar azummatar ranar Arfa ga wanda ba wurin Arfa ba, azumin da akace Annabi muhammad S.A.W yace za’a karkare ma mutum zunubin shekara biyu Idan yayi shi.

Shi dai wannan taron an yi shine a fadar Mai alfarma sarkin musulmi da ke sokoto,alokacin wani taron tattanawa ta musamman da ya gayyaci wasu malumman jihar sokoto, kungiyoyin addini, limamai da sauran su, tare da hadin guiwar hukumar zakka da wakafi ta jihar sokoto wadda malam Muhammad lawal maidoki ke jagorantaka,domin sarkin musulmi ya tattauna da su akan hanyoyin da zaa inganta ayukkan karbar zakka a jihar sokoto, domin taimakawa Alummar musulmi.

Shi dai riginginmun sha’anin ganin wata ko daukar azumi ko sallah a Nigeria ba bakon abu ne ba, duk da kokarin da Sarkin musulmi da shugabannin addinin musulunci ke kokarin shawo kanshi, a baya bayannan an samu hadin kan mafi yawan Musulmin kasar nan wajen daukar azumi ko ajewa.

Akwai bukatar majalisar koli kan harkokin addinin musulunchi a Nigeria karkashin sarkin musulmi ta shirya wani taro na musamman wanda zai hada dukkan bangarorin musulmi, shugabannin kungiyoyin addinin musulunchi, sarakuna ,kwamitin ganin wata na kasa, da sauran masu ruwa da tsaki a shaanin ganin wata da ma sauran lamurran da suka shafi alummar musulmi a wannan kasar domin samun mafita.

[ad_2]

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riƙaƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 ƙirar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...