Sarkin Bauchi Ya Dauki Nauyin Karatun Wasu Marayu Da Marasa Karfi

A cigaba da manufofin sa na ganin harkokin ilimi na bunkasa,musamman ma mata da matasa masu hali da talakawa sun samu ilimi a kasar Bauchi, Mai Martaba Sarkin Bauchi Injiniya Alh Dr Rilwanu Sulaiman Adamu, ya dauki dawainiyar wasu Yara marayu da kuma ya’yan mutane marasa karfi cikin al’umma. Inda Mai martaba Sarkin Bauchi, ya saya musu dukkanin kayan da dan makaranta ke bukata domun neman ilimi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Mai Martaba Sarkin Bauchi ya dinka wa yaran kayan makaranta, an saya musu littatafai, takalma, Jakunkunan makaranta kamar yadda kowane uba ke yi wa ya’yansa.

Yaran za su ci gaba da gudanar da karatun su ne karkashin kulawar Mai Martaba Sarkin Bauchi, inda zai ci gaba da daukar nauyin karatun su daga makarantan firamare yanzu har matakin karatu na gaba.

Hotuna Daga Nasiru Muazu

More from this stream

Recomended