Sarkin Bagaji Odo da ke ƙaramar hukumar Omala a jihar Kogi, David Akpa, wanda aka sace a ranar Litinin da ta gabata, ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar Omala, Gift Idoga, ya fitar a madadin shugaban, Edibo Mark, ranar Asabar.
A cewar sanarwar, “an ceto Sarkin ne bayan haɗin gwiwar jami’an tsaro, masu farauta da ƙungiyoyin sa-kai, karkashin jagorancin shugaban ƙaramar hukumar.”
An tunatar da cewa an yi garkuwa da Sarkin Bagaji Odo, David Akpa, a ranar 1 ga watan Satumba, 2025, inda aka yi awon gaba da shi zuwa dajin.
Sanarwar ta ƙara da cewa tun bayan faruwar lamarin, shugaban ƙaramar hukumar Omala ya kafa rundunar haɗin gwiwa da ta haɗa da ‘yan sanda, sojoji, masu farauta da sa-kai. Har ma shugaban ya halarci aikin bincike a kalla sau biyu.
Sarkin dai an ce an ceto shi ne da safiyar Alhamis, kuma yanzu haka yana samun kulawa ta musamman a gidan shugaban ƙaramar hukumar.
Sarkin Bagaji Odo Da Aka Sace A Kogi Ya Shaƙi Iskar Ƴanci
