
Sulaiman Nazif Gamawa tsohon mataimakin shugaban jam’iyar PDP na ƙasa ya sanar da ficewarsa daga jam’iyar PDP.
Nazif wanda tsohon sanata ne da ya wakilci al’ummar mazabar arewacin Bauchi ya sanar da komawarsa jam’iyar SDP daga PDP a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Sanatan ya ce ya ɗauki matakin ne na komawa SDP domin samar da wani bigire mai ƙarfi da zai ƙarfafa ginshikan dimakwaradiya a Najeriya.
A yan kwanakin nan ana cigaba da samun jiga-jigan ƴan siyasa da suke komawa jam’iyar ta SDP tun bayan da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya koma jam’iyar daga jam’iyar APC.