
Ogoshi Onawo, Sanata dake wakiltar mazabar kudancin Nasarawa a majalisar dattawan Najeriya ya sanar da ficewarsa daga jam’iyar PDP.
A wata wasika mai dauke da kwanan watan 10 ga watan Janairu da ya aikewa shugaban jam’iyar PDP na mazabar Galadimawa a karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa Onawo ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyar ba tare da bata lokaci ba.
” Na dauki wannan matakin a kashin kai na bayan da nayi duba na tsanaki,”a cewar wasikar.
Onawo ya godewa shuagabanci da kuma mambobin jam’iyar kan damar da suka bashi ta wakiltar al’umma.
Sanatan ya yi wa jam’iyar ta PDP fatan alheri anan gaba.
Duk da cewa Onawo bai bayyana jam’iyar da zai koma ba a yan kwanakin nan ana alakanta shi da jam’iyar adawa ta ADC.

