Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafin cin zarafi kan Akpabio a Majalisar Dattawa

Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta gabatar da ƙorafi kan cin zarafi da ta yi zargin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi mata.

Sanata Natasha ta miƙa ƙorafin ne a zaman majalisar da aka gudanar ranar Talata, bayan dawowar majalisar daga hutu.

Tun da farko, majalisar ta bayyana cewa ba ta bincike kan wannan zargi domin babu wata takardar ƙorafi da aka shigar da ta shafi Akpabio a gaban majalisar.

A safiyar Talata, an hango Sanata Natasha tare da mijinta a harabar majalisar, yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Abuja, inda masu zanga-zangar ke neman Shugaban Majalisar Dattawa ya yi murabus.

More from this stream

Recomended