
Ibrahim Musa, tsohon sanata da ya wakilci mazabar arewacin jihar Niger karkashin jam’iyar CPC ya rasu.
Musa wanda lauya ne da ya shafe shekaru 17 yana aiki ya wakilcin al’ummar yankinsa a majalisar dattawa daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Ana daukar marigayin a matsayin dan gani kashenin tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari.
A wata sanarwa ranar Alhamis, Abubakar Usman sakataren gwamnatin jihar Niger ya sanar da rasuwar marigayin.
Usman ya ce tsohon dan majalisar dattawan ya mutu ne a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ya ce rasuwar marigayin babban rashi ne ba wai ga masarautar Kontagora kadai ba a’a ga bakin dayan al’ummar jihar Niger.