
Godiya Akwashiki sanata dake wakiltar mazabar arewacin jihar Nasarawa majalisar dattawa ta Najeriya ya mutu a kasar India bayan da ya yi fama da jinya.
Akwashiki ya rasu yana da shekaru 52 a duniya.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN ya rawaito wata majiya ta iyalan marigayin na cewa dan majalisar dattawan ya mutu ne a ranar 31 ga watan Disamba shekarar 2025 a wani asibiti inda yake jinya.
Majiyar ta bayyana cewa mutuwar tasa wani babban rashi ne ga arewacin jihar Nasarawa dama daukacin jihar baki É—aya.
Ya kara da cewa marigayin ya bambanta da sauran yan siyasa idan aka yi duba da ya yadda ya sadaukar da kai wajen samar da cigaba, abubuwan more rayuwa da kuma tallafawa da kayan sana’o’i a tsawon lokaci da ya shafe yana siyasa
Akwashiki na wakiltar mazabar a majalisar dattawan karkashin jam’iyar SDP gabanin zamansa dan majalisar dattawa a shekarar 2019 ya rike muÆ™amin shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar kafin daga bisani ya zama mataimakin shugaban majalisar dokokin.

