
Okey Ezea, Sanata mai wakiltar arewacin Enugu ya mutu yana da shekaru 62 a duniya.
A cikin wata sanarwa da dansa, Jideofor Ezea ya fitar ya ce sanatan ya mutu a wani asibiti mai zaman kansa dake Lagos da misalin karfe 11:07 na daren ranar 18 ga watan Nuwamba baya gajeriyar rashin lafiya.
Ezea ya taba rike shugabancin kwamitin da’a da korafin jama’a na majalisar har ila da kuma muƙamin mataimakin shugaban kwamitin gidaje da bunkasa birane na majalisar da kuma shugaban kwamitin al’adu na majalisar.
Sanatan na daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyar APC a jihar Enugu kafin daga bisani ya koma jam’iyyar Labour party inda ya tsaya takarar sanata a zaɓen shekarar 2023.

