Sakataren gwamnatin jihar Bauchi ya yi murabus

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya amince da murabus ɗin sakataren gwamnatin jihar, Barista Ibrahim Muhammad Kashim.

Wata sanarwa da mai bawa gwamnan shawara kan kafafen yaɗa labarai, Gidado Ahmad ya fitar ta ce murabus din ya fara aiki nan take.

A cewar sanarwar tuni aka umarci shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Aminu Gamawa da ya cigaba da gunadar da ayyukan Kashim har ya zuwa wani lokaci.

Gwamna Bala ya godewa Kashim kan hidimtawa jihar da ya yi a iya lokacin da ya kwashe yana riƙe da mukamin.

More from this stream

Recomended