Sace-sacen motoci ya yawaita a Adamawa—Ƴan sanda

Ana ci gaba da samun karuwar sace-sacen motoci a jihar Adamawa, kamar yadda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana haka ne a wata sanarwa a safiyar ranar Asabar, tana mai sanar da jama’a kan karuwar satar motoci, musamman a kananan hukumomin Yola ta Arewa da Yola ta Kudu da kuma Girei.

Sanarwar ta fito ne daga kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Suleiman Nguroje.

Ya ce a wani mataki na dakile tashe-tashen hankulan, rundunar za ta fara gudanar da bincike mai zurfi a yankunan da lamarin ya shafa wanda ka iya janyo cunkoson motoci.

“Saboda haka kwamishinan ‘yan sanda ya yi kira ga masu ababen hawa da su fahimce su domin matakin na kare lafiyarsu da tsaron lafiyarsu ne,” in ji Nguroje.

Ya yi kira ga jama’a da cewa za su iya kiran  rundunar ‘yan sanda a wadannan lambobin 08089671313, idan wani lamari ya faru.

More from this stream

Recomended