Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya ce sabuwar dokar zabe da ake ci gaba da cece-kuce kanta, za ta iya haddasa ruduni ne kawai da kashe makudan kudade, don haka ya sa shugaba Buhari ba zai sanya mata hannu ba.
A yayin wata zantawa da wani gidan rediyo a Kano, Ministan ya ce dokar za ta kuma kara ta’azzara kalubalen rashin tsaro, haka kuma ba ta wakilcin ra’ayin akasarin ‘yan Najeriya.
In za’a iya tunawa shugaba Buhari ya ki amincewa da sanya hannu kan dokar bayan da majalisar dokoki zartar da ita, inda ya rubuta wasika ga majalisar yana baiyana dalilan jingine dokar.
An sami ‘yar muhawara a tsakanin ‘yan majalisar inda su ka ce za su tuntubi jama’a a hutun da su ka shiga yanzu in sun dawo su dauki matsayar amincewa da dokar ko akasin hakan.
Da ya juya kan kudaden da aka kwato daga kasashen waje wadanda barayin gwamnati suka sace, Malami ya ce ana amfani da su wajen aiwatar da manyan ayyuka a kasar, yaki da ayukan ta’addanci da kuma gudanar da shirye shiryen ayyukan jin kai.
Malami ya ambato babbar hanyar Legas zuwa Ibadan da babbar hanyar Kano zuwa Abuja da gadar Neja ta biyu cikin wasu manyan ayyuka da aka yi da wadannan kudaden.
ya kuma kara da cewa an yi amfani da kudaden da aka kwato wajen shirye-shirye na taimakon al’umma da suka hada da ciyar da makarantu da kuma ba da tallafi na N-Power.
Malami ya bayyana cewa yakin da aka yi da ayyukan cin hanci da rashawa a kasar bai zai bar duk wani jami’in gwamnati da aka samu da laifi ba, saboda sha’anin cin hanci da rashawa bai san mukami ba.