Sabuwar cuta ta ɓulla a Kaduna

Akalla yara 10 ne ‘yan tsakanin shekaru uku zuwa 13 aka ce an kwantar da su a asibiti sakamakon bullar wasu cututtuka masu ban mamaki a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jema’a a jihar Kaduna.

An gano cewa barkewar cutar ta tilastawa rufe makarantun firamare da sakandare da dama yayin da ake ci gaba da bincike.

Shugaban karamar hukumar Yunana Barde, wanda ya tabbatar da bullar cutar, ya ce baƙuwar cutar ta bulla ne a daren Laraba.

Barde ya zanta da manema labarai a babban asibitin Kafanchan ranar Alhamis.

Sai dai ya bukaci mazauna yankin da kada su firgita saboda ana kokarin shawo kan cutar yayin da ya yaba wa babban asibitin da ya samar da cibiyar keɓewa na ɗan lokaci ga waɗanda ake zargi da kamuwa da cutar.

Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da Daraktan Kiwon Lafiya na Babban Asibitin, Dakta Isaac Nathaniel, ya ce ana daukar matakan farfado da mutane 10 da ake zargi da kamuwa da cutar a lokacin da aka kwantar da su.

Ya kuma kara da cewa, tun daga lokacin ne aka tattara samfurin mutane 10 da ake zargin sun kamu da cutar don ci gaba da bincike kan wannan bakuwar cutar.

More from this stream

Recomended