Ruwan Sama Mai Karfi YaYi Sanadiyyar Rushewar Gidaje Masu Yawa A Jihar Katsina

Ruwan sama mai ‘karfi da ya ɗau awanni yana sauka a ‘karshen makon da ya gabata ya yi sanadiyyar rushewar gidaje 184 a yankuna takwas da ke Karamar Hukumar Kurfi, Jihar Katsina.

Majiyar Sarauniya ta samu rahoton cewa bayan rushewar gidajen, ruwan ya kuma yi awon gaba da gonannakin mutane.

Yankuna takwas ɗin da ibtila’in ya auka wa su ne: Wurma, Birchi, Tsauri, Kofar Fada, Nasarawa, K’ofar Yamma, Sabuwar Unguwa da K’ofar Arewa.

Mutanen yankin sun ce an fara ruwan da misalin ‘karfe 1:15 na dare sannan ya tsaya da misalin ‘karfe 12 na rana. Hakan shi ya sa kogin da ke makwabtaka da su yayi ambaliyar da ta yi silar rushewar gidaje.

Wani ganau da ya nemi kada a ambaci sunanshi ya ce: “Gidaje 20 sun rushe a Wurma, 32 a Birchi, 23 a Tsari, 11 a K’ofar Fada, 19 a Sabuwar Unguwa, 32 a K’ofar yamma, 14 a K’ofar arewa, sannan kuma gidaje 43 a yankin Nasarawa.”

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riƙaƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 ƙirar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...