Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna Ta Yi Alkawarin Zakulo Wadanda Suka Kashe Jami’an ta

[ad_1]

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce kokarin da take yi na kwakulo wasu ‘yan bindiga ne ya sa aka kashe mata jami’anta guda hudu a lokacin da suka je yin wani aiki a unguwar Rigasa a garin Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar DSP Yakubu Sabo, wanda bai yadda wakilin Sashen Hausa ya dauki muryarsa ba, ya tabbatar cewa yanzu haka rundunarsu ta kara aikewa da karin jami’ai a wurin da ‘yan bindigan suka yiwa jami’an da suka kashe kwantan bauna. Sai dai har yanzu ba’a kama mutum ko daya cikin wadanda suka aikata wannan ta’annati ba.

DSP Sabo ya ce rundunar ta yi alkawari kama dukannin tsagerun dake tada kayar baya a jihar, walau barayin mutane ko kuma masu tada hayaniya a wasu bangarorin jihar.

Birgediya Muhammad Kabiru Galadanci mai murabus ya ce akwai lauje cikin nadi game da wannan batu. Yace kafin su tashi zuwa Jankasa kamata ya yi su aika da ‘yan sandan farin kaya da zasu taimaka wajen tara bayanai. Baicin hakan akwai ofishin ‘yan sanda a Rigasa kuma sun san wasu jami’an su na zuwa. Amma ayar tambaya nan ita ce yaya su ‘yan bindigan suka san za su zo, har suka yi masu kwantan bauna? A cikin jami’an tsaron akwai bara gurbi da yawa dake kewaya su tsguntawa miyagun mutanen duk abun da aka shirya za’a yi. Ya ce da jin labarin ya tabbata wani cikin ‘yan sandan ya bada labarin zuwan su saboda za’a bashi kudi dubu hamsin ko dubu dari.

Kwanakin baya, a wani kauyen dake kusa da Rigasa aka sace wani malamin addinin Musulunci Shaikh Ahmed Albarkawi wanda ya kwashe ‘yan kwanaki kafin barayin su sako shi.

A saurari rahoton Isa Lawal Ikara

[ad_2]

More News

Obasanjo ya kai wa Remi Tinubu ziyara

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara ga, Oluremi Tinubu mai ɗakin shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu . Obasanjo ya ziyarci matar shugaban ƙasar a...

Shehin Musulunci ya nemi masu kuɗi da su raba wa talakawa naman Salla

Mataimakin Babban Limamin Masallacin Yobe da Cibiyar Musulunci, Malam Mohammad Ali Goni Kamsulum, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su rika...

Ƴansandan sun yi artabu da ƴanbindiga a Abuja

Jami’an ‘yan sanda daga babban birnin tarayya Abuja sun kashe wani dan bindiga tare da cafke uku a wani samame da suka kai.Ƴan sandan...

An wallafa sunaye da hoton fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Suleja

Hukumar NCoS dake lura da gidajen gyaran hali da tarbiyya ta fitar da sunaye da kuma hotuna na ɗaurarrun da suka tsere da gidan...