Rundunar ’Yan Sanda Ta Kama Mutum 10 Kan Fashi Da Satar Shanu A Jihar Neja

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja ta kama mutum 10 da ake zargi da aikata fashi da makami, tashin hankali, mallakar makamai masu haɗari da kuma satar shanu a sassa daban-daban na jihar.

Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana a wata sanarwa cewa an kama su ne a jerin samamen da tawagar sintiri da jami’an sashen Tudun-Wada da Cibiyar ’Yan Sanda ta Minna suka gudanar.

A cewarsa, an cafke wasu matasa biyu—Habibu Isyaku mai shekara 20 da Musa Yakubu mai shekara 18—akan babur a kan Western Bye-Pass a ranar 17 ga Nuwamba, inda aka gano bindiga ta gida a tare da su. Ya ce sun kasa bada cikakken bayani kan makamin.

An gurfanar da su kan tuhumar hadin baki wajen aikata laifi, tashin hankali, mallakar makamai masu haɗari da kuma amfani da kayan maye.

Haka kuma, Abiodun ya ce an kama wasu mutum biyar a wani samame da aka kai a wuraren da ake zargi a Sayako, Tudun-Natsira, Abdul Salam Quarters da Baida a ranar 14 ga Nuwamba. An kama su da tabar wiwi, wuka, doguwar aska da sauran kayan maye.

Rundunar ta kuma kama wasu mutum uku da ake zargi da karɓa da sayar da shanun da aka sace a yankin Ibeto da ke karamar hukumar Magama. An gano shanu takwas a hannunsu, yayin da ake neman wasu biyu—Bashar Sani da Ibrahim Tasiu—da suka tsere.

Abiodun ya ce bincike na cigaba domin gano sauran masu hannu da sauran shanun da aka sace.

More from this stream

Recomended