Daruruwan ‘yan daba dauke da muggan makamai sun shiga hannun jami’an tsaro a yayin zaben cike-gurbi da ake gudanarwa a Jihar Kano.
Kwamishinan hukumar INEC na jihar, Ambasada Abdu Zango, ya tabbatar wa manema labarai cewa jami’an tsaro sun kama wadannan ‘yan daba ne a lokacin da suke kokarin shiga Bagwai, inda ake kada kuri’a.
Zango ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan daban a Shanono sun kusan kawo tarnaki ga jigilar kayan zabe, sai da jami’an tsaro suka shawo kan lamarin suka dawo da komai dai-dai.
Ya ce, duk da cewa Shanono na daga cikin wuraren da ake ganin tashin hankali kan iya faruwa a lokacin zabe, zuwan jami’an tsaro ya tabbatar da cewa zaben yana tafiya cikin kwanciyar hankali da lumana.
Rundunar Tsaro Ta Kama Daruruwan ‘Yan Daba A Zaben Cike-Gurbi Na Kano
