Rundunar Sojan Saman Najeriya Ta Kashe Abu Asad Jigo A Ƙungiyar Boko Haram

Bangaren sojan sama na rundunar Operation Hadin Kai ya sanar da kisan Abu Asad ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Boko Haram.

Ƙarin ƴan ta’ada da dama aka bada rahoton sun mutu a harin da jiragen yaki suka kai musu a maboyar su dake Tagoshe a tsaunukan Mandara.

Edward Gabkwet daraktan yaɗa labarai na Rundunar Sojan Saman Najeriya shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Asabar a Abuja.

Gabkwet ya ce an kai farmakin ne a ranar Juma’a inda ya ce harin na daga cikin mafi nasara da bangaren sojan sama na rundunar Operation Hadin Kai ya kai a ƴan kwanakin nan.

Ya ce kafin kai harin sojojin saman sun ga ƴan ta’adda kusan sama da ɗari tare da wasu motocin yaƙi huɗu suna ta tattaunawa suna raha a tsakanin su a wurin dake da wasu gine-gine uku.

“Biyo bayan kai harin biyu daga cikin ginin sun rushe tare da dukkanin motocin yaƙin da aka lalata su”

“Akwai alamu dake nuna cewa Abu Asad wanda ƙusa ne a Boko Haram bangaren Ali Ngulde da kuma sauran yan ta’ada kamar su Ibrahim Nakeeb, Mujaheed Dimtu, Mustafa Munzir da sauransu na daga cikin ƴan ta’adda da dama da aka kashe a harin.” a cewar sanarwar.

More from this stream

Recomended