Rundunar Ƴan Sanda ta Babban Birnin Tarayya ta kama wani mutum mai shekaru 32 da ake zargi da yunƙurin samo alburusai domin ƙungiyoyin ’yan bindiga da ke aiki a Jihar Zamfara.
Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa an kama mutumin, Ahmed Abubakar, ɗan asalin Gusau wanda mazaunin Anguwan Dodo a Gwagwalada ne ranar 7 ga Disamba misalin ƙarfe 3:30 na yamma bayan samun sahihin bayanan leƙen asiri daga ofishin Mabushi.
Majiyoyin sun ce Abubakar ya nemi wani soja, Cpl. Yusuf Mohammed, ya taimaka masa da samun alburusai 1,000 domin mika su ga ’yan bindiga a Zamfara, tare da yi masa alƙawarin lada.
A lokacin bincike, Abubakar ya ce yana aiki ne bisa umarnin kawunsa, Ahmed Yakubu, wanda ya tsere.
Ƴan sanda sun samu kuɗi naira 170,100 tare da wanda ake zargin, wanda ake zaton a cikin kuɗin da aka ware domin sayen haramtattun makamai ne.
Rundunar Ƴan Sandan Abuja Ta Cafke Mutumin Da Ake Zargi Da Ƙoƙarin Safarar Alburusai Wa Ƙungiyoyin Ƴan Bindigar Zamfara

