Rugujewar gini bayan an yi ruwan sama mai ƙarfi ya yi ajalin mutane 2 a Kano

Akalla mutane biyu ne aka ruwaito sun mutu a wani gini da ya rufta a Nomansland da ke karamar hukumar Fagge a jihar Kano, tare da ceto wasu biyu da ransu. 

An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na safiyar ranar Alhamis, biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abudullahi, ya tabbatar da cewa, jami’an ceto sun yi nasarar ceto wasu mutane biyu da aka kwantar da su a asibiti, yayin da aka ci gaba da aikin fito da gawarwakin wadanda suka mutu.

Lamarin ya biyo bayan mummunar barnar da ambaliyar ruwar ta yi a jihar Kano.

A halin da ake ciki kuma, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano ta bayar da rahoton a ranar Larabar da ta gabata cewa, ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 31 tare da lalata gidaje 5,280 a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka ƴanbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...