Rikicin Ukraine: Rasha za ta kai karar FIFA da UEFA kotu

Hukumar Kwallon Kafar Rasha ta ce za ta garzaya kotun da’ar wasanni (CAS), don kai koke game da dakatar da ita da kungiyoyin ta shiga harkokin kwallon kafa.

A ranar Litinin ne hukumomin kwallon kafa na Fifa da Uefa suka sanar da dakatar da Rasha da kungiyoyin ta na kwallon kafa shiga kowace irin gasa har sai yadda hali ya yi, saboda kutsawa Ukraine.

To amma a martanin Hukumar Kwallon kafar kasar, ta ce za ta shigar da kara a kotun da’ar wasannin don kalubalantar matakin.

A yanzu Rasha na son a ba tawagar ta damar buga wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya, a kuma kyale tawagar matan kasar zuwa gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2022 da za a yi a Ingila.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Spartak Moscow an kore ta daga gasar Zakarun Turai ta Europa, wanda hakan ke nufin abokiyar karawar ta RB Leipzig ta tsallake zuwa zagayen quarter-finals.

Sanarwar Rasha ta ce ”a iya saninmu Fifa da Uefa ba su da hurumi bisa doka na hana Rasha shiga harkar kwallon kafa.”

Sanarwar ta kuma kara da cewa ”kuma ba a bamu damar kare kanmu ba, wanda hakan ya saba wa yancin wanda ake tuhuma.”

Fifa da Uefa sun dauki matakin ne bayan da Rasha, tare da goyon bayan Belarus, ta kutsa tare da kai hare-hare Ukraine makon da ya wuce.

Rasha ta ce za ta nemi a umurci hukumomin su janye dakatarwar, ko kuma a dakatar da gudanar da gasannin da suke ciki kafin a samu maslaha.

More from this stream

Recomended