Rikicin Sudan: Jami’an tsaro sun ‘far wa masu zanga-zanga’ | BBC Hausa

Dakarun Sudan sun kai wani hari kan masu zanga-zanga da ke fafutukar kafa mulkin demokradiyya wadanda ke gaban shalkwatar sojojin kasar a Khartoum.

An rika jin karar harbin bindiga, kuma wata majiya ta likitocin kasar ta ce akalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu bayan gomman da suka sami raunuka.

Wata majalisar sojoji ce ke mulkin kasar tun bayan da aka hambarar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar al-Bashir a watan Afrilu.

Kungiyoyin da ke zanga-zangar na neman a mika mulki ga wata gwamnatin farar hula, sun kuma ce za su yanke dukkan wata hulda da gwamnatin sojojin kasar, bayan kira da ta yi a fara yajin aiki na gama gari.

Babban kwamitin Likitocin Sudan, wanda ke cikin kungiyoyin masu zanga-zangar ya ce an kashe mutum 13, sannan kwamitin ya ce “an raunata wasu mutanen masu yawa”.

  • An dakatar da tattaunawar mika mulki a Sudan
  • An kashe masu zanga-zanga a Sudan

Halin da ake ciki a yanzu

Jami’an tsaro sun kai wani samame kan masu zanga-zanga da sanyin safiyar Litinin, inji masu fafutukar suka kafa mulkin demokradiyya.

Hakkin mallakar hoto
AFP/Getty Images

Image caption

Masu zanga-zanga sun rika kona tayoyi aa wani kokarin dakatar da samamen da jami’an tsaro ke kai wa

Kakakin majalisar sojoji da ke mulkin kasar, Laftana Janar Shams al-Din Kabbashi ya ce jami’an tsaron sun kai samame zuwa wani wuri da “aka dade ana ruruta wutar rikicin”.

Sai dai wani dan jarida mai aiki a birnin Khartoum ya shaida wa BBC cewa ” na kirga gawawwakin masu zanga-zanga guda 11 sannan na ga gawawwakin sojoji guda 16.”

Ya kuma kara da cewa “sojoji da farar hula na kai wa juna farmaki.”

Yadda rikicin ya samo asali

Hakkin mallakar hoto
AFP

  • 19 ga Disamba 2018 – rikici ya barke bayan karin kudin man fetur da biredi da gwamnati ta yi
  • 22 ga fabrairu 2019 – Shugaba al Bashir ya rusa gwamnatinsa
  • 24 ga Fabrairu – Zanga-zanga ta ci gaba, jami’an tsaro sun rika harbi da bindiga
  • 6 ga Afrilu – Masu zanga-zanga sun fara zaman dirshan a shalkwatar sojojin kasar
  • 11 ga Afrilu – Manyan hafsoshin sojojin kasar sun bayyana hambare al Bashir daga mukaminsa
  • 20 ga Afrilu – An fara tattaunawa tsakanin gwamnatin sojoji da masu fafutuka
  • 13 ga Mayu – Harbe-harbe a gaban shalkwatar sojojin kasar ya yi sanadin mutuwar mutum shida
  • 14 ga Mayu – Wakilan gwamnatin soja da na fararen hula sun cimma yarjejeniyar mika mulki na shekara uku masu zuwa
  • 16 ga Mayu – An dkatar da tataunawa bayan da gwamnatin soja ta nemi a kawar da asu shingaye a Khartoum
  • 3 ga Yuni – Masu fafutuka sun sanar da jingine tattaunawar da suke yi da majalisar sojojin kasar, kuma sun tuhume su da amfani da karfin soji domin tarwatsa su

More from this stream

Recomended