Rikici ya kunno kai a PDP a Kano

[ad_1]

PDP Nigeria

Bayan sauke shugabannnin jam’yyar PDP da uwar jam’iyyar ta kasa ta yi, wasu jiga-jigan jam’iyyar a Kano sun nuna rashin gamsuwarsu da wannan matakin.

Da alama tsugune ba ta kare ba a siyasar Kano, domin wannan matakin ya janyo rarrabuwar kawuna tsakanin jagororin jam’iyyar PDP a Kano.

A bangare daya, Mallam Ibrahim Shekarau da Aminu Wali da Bello Hayatu sun ce ba za su amince da matakin uwar jam’iyyar ba.

Mallam Ibrahim Shekarau ya bayyana matsayarsu a wata hira da yayi da maneman labarai.

“Ni Ibrahim Shekarau, a madadi na da sauran jagorori da shugabanni na jam’iyyar PDP ta jihar Kano, na godiya ga magoya bayan jam’iyyar saboda hakuri da biyayya da ake nunawa ga jagorancin jam’iyya.”

‘A dakatar da sauya shugabannin PDP’

Mallam Shekarau ya ce suna sane da matakan da uwar jam’iyyar PDP ta dauka wadadnda har suka kai ga cewa ta sauke shugabanninta a jihar Kano.

“Muna kara tabbatar wa mutane cewa kafin a dauki wannan matakin, wasu masu kishi da son cigaban jam’iyya sun kai kara, kuma kotu a Kano ta bayar da umarni cewa a dakatar da duk wani yunkuri na sauke shugabanni.”

Image caption

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje

Akwai rarrabuwar kawuna tsakanin bangaren Shekarau da na Kwankwaso, wadanda ba tun yau ba sun kasance abokan hamayya a siyasar Kano.

Mallam Ibrahim Shekarau ya kuma ce, “Muna nan muna bibiyar hakkin dukkan dan PDP da ke jihar Kano, kuma ba za mu bari a karya dokar jam’iyya ba.”

Rahotanni na cewa rikicin jam’iyyar ta PDP na bazuwa zuwa wasu jihohin kamar Kogi, da Binuwai da Sokoto.

Idan ba a iya magance wannan rikicin ba, musamman a wannan lokacin da ake tunkarar zabukan shekarar 2019, PDP na iya tafka asara a siyasance.

Ita kuma jam’iyya mai mulki a jihar Kano, APC za ta ci gajiyar wannan rikicin da ke son dabaibaye PDP Kano.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...