An bai wa hamata iska a tsakanin masu neman tsayawa takara a inuwar jam’iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara ta Najeriya.
Rikicin ya barke ne dazu da rana bayan da aka gaza cimma matsaya a kan tsarin da za a bi wajen zaben ‘yan takarar na jam’iyyar APC.
Kwamitin zaben da uwar jam’iyyar ta kasa ta tura zuwa jihar dai ne ya tsara yadda za a gudanar da zaben, amma daga bisani aka samu sabani a tsakanin ‘yan takarar inda wani bangaren masu takarar ke ganin tsarin da ake son a bi wajen zabar ‘yan takarar bai dace ba.
Shi dai kwamitin zabe na jam’iyyar ya kawo shawarar a gudanar da zaben bisa tsarin ‘yar tinke kuma dole a tabbatar duk wanda zai yi zaben da sunayensu a cikin rijistar jam’iyya.
Kazalika kuma a kawo wasu mutane daban wadanda za su yi aikin zaben.
Wadannan sharuddan ne ba suyi wa bangaren masu hamayya da dan takarar da gwamna ke goyawa baya dadi ba abin da ya haifar da rikici har aka dambace.
Yanzu haka dai kura ta lafa, amma kuma har kawo yanzu ba a cimma wata matsaya ba, don haka ba a fara zaben ba.
Har yanzu dai ana zaman jiran raba kayan zabe a jihar Zamfara. Nan Hotel din City King ne, inda sakatariyar kwamitin zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC yake.