An samu hargitsi a wani bangare na jihar Lagos ranar Alhamis ya yin da wasu batagari da ake kyautata zaton yan bangar siyasa ne suka kai hari a a wuraren da ake yin zaben fid da gwanin na yan takarar majalisar kasa karkashin jam’iyyar APC.
A wurare da dama yan bangar siyasan sun isa tashoshin zabe tamkar wasu kwamandodin soja inda suka riƙa harbi sama a kokarinsu na tarwatsa mutane dake kan layuka ko kuma ma korarsu daga harabar wurin zaben baki daya.
A wurare kamar su Lagos Island,Mainland, Ikosi a karamar hukumar Kosofe da kuma Epe mutane hudu aka rawaito sun mutu kusan mutum daya kenan a kowane wuri, mutanen sun mutu ne sakamakon harbin kan me uwa da wabi da yan bangar siyasa suka riƙa yi.
Tsohon mai neman takarar shugabancin karamar hukumar Kosofe , Ibrahim Mustapha ya tsallake rijiya da baya lokacin da wasu batagari suka farmasu shi da magoya bayansa duk da cewa an samu nasarar ceto shi batagarin sun samu nasarar yi masa munanan raunuka.