Rikici ya ɓarke a Abuja inda ƴan jari bola suka kashe mutane 3

Rahotanni sun ce an kashe mutane uku da suka hada da mata biyu da yaro daya a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan iskan gari da ake kira baban bola da mazauna unguwar Byazhin a Kubwa a karamar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya Abuja.

Wata shaidar gani da ido, wacce ta bayyana kanta da Jessica Adam, ta shaida cewa, wani baban bola ya yi yunkurin satar tukunyar miya ta wata mata, amma abin ya ci karfinsa kuma an lakada masa duka bayan matar ta sanar da makwabta da masu wucewa.

Baban bolan wanda ya harzuka ya tafi ya tara ‘yan iskan da suka dawo da misalin karfe 8 na dare dauke da makamai da suka hada da adduna, kulake, da duwatsu, suka fara kai wa mazauna garin hari ba kakkautawa, inda suka kashe matar da aka sace wa tukunyar miyar.

A harin, an kashe wasu mutane biyu, mace da wani yaro matashi, wadanda aka ruwaito cewa masu wucewa ne.

A halin da ake ciki, kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya ci tura, domin an kasa samun lambarta.

More from this stream

Recomended