Rijiyoyin mai guda biyar sun kama da wuta a Ondo

Wasu rijiyoyin mai guda biyar sun kama da wuta a jihar Ondo daya daga cikin jihohin dake da arzikin man fetur a Najeriya.

Bayanan da jaridar The Cable ta tattara sun nuna cewa gobarar da ta tashi ranar Alhamis a yankin Ajegunle Ikorigho ta kuma shafi wani ɓangare na Ajumole.

Rijiyoyin man da gobarar ta shafa sun hada da Isan West Field,Parable field, Malu field, Ororo da kuma Opokaba.

Har ila yau gobarar ta yadu zuwa yankunan al’ummar dake zaune a Ikorigho, Ajegunle-Ikorigho, Zion Ikorigho, Iluayo, Kendo Ayeren da kuma Ehinmoghan-Ikorigho.

Wata majiya ta fadawa jaridar cewa kamfanin mai na Chevron Nigeria Limited shine ya mallaki rijiyoyin amma binciken da jaridar ta gudanar ya gaza tabbatar da haka.

Ya zuwa lokacin da jaridar ta wallafa labarin ba a iya gano dalilin da ya haddasa tashin gobarar ba.

More from this stream

Recomended