Ribadu ya miƙawa gwamnatin Kaduna mutane 58 da aka kuɓutar daga hannun masu garkuwa da mutane

Mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya miƙawa gwamnatin jihar Kaduna wasu mutane 58 da aka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar.

Da yake magana a wurin taron miƙa mutanen a ranar Talata Ribadu ya ce an ceto mutanen a wani farmaki da rundunar sojan Najeriya ta jagoranta da kuma sauran hukumomin tsaro.

Ya ce waɗanda aka kuɓutar din sun haɗa da mata 28 da kuma maza 24 sai kuma ƙananan yara 6 kuma an kuɓutar da su daga wurare daban-daban dake cikin jihar ta Kaduna.

Ribadu ya ce an yi aikin ceton ne domin dawo da zaman lafiya, tsaro da kuma al’amuran yau da kullum su cigaba da gudana kamar yadda suke a baya a Najeriya.

Sani Kila shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kaduna ya godewa Ribadu kan yadda ya tabbatar da mutanen sun dawo gida domin cigaba da rayuwa a cikin iyalansu.

More from this stream

Recomended