Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da ƴan ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami’an ƴan sanda da kuma sojoji suna ɗaukar bindigogi daga wuraren aikinsu su sayarwa ɓatagari.

Ribadu ya bayyana haka ne a wurin bikin lalatata bindigogi da cibiyar yaƙi da  bazuwar ƙananan makamai ta ƙasa ta shirya a Abuja.

Bikin ya gudana ne barikin sojojin ta Muhammad Buhari Cantonment dake Giri a Abuja.

Ribadu yayi allawadai da jami’an tsaron wanda suke taimakawa ƴan ta’adda da kuma sauran ɓatagari ta hanyar samar musu da bindigogi.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin bindigogin da ake amfani da su wajen aikata laifuka a kasar nan asalinsu na gwamnati ne.

Ya ce lalata bindigogin da aka gano dama wasu bindigogin da suka tsufa ya nuna irin muhimmancin da gwamnatin tarayya ke nunawa wajen samarwa da ƴan Najeriya makoma mai kyau.

More from this stream

Recomended