
Mai bawa shugaban kasa, Bila Ahmad Tinubu shawara kan harkokin tsaro , Mallam Nuhu Ribadu ya gana da shugabannin rundunar sojan Najeriya a hedkwatar hukumar dake yaki da ta’addanci.
Duk da cewa a bayyane dalilin da ya sa aka yi ganawar ba wasu majiyoyi sun bayyana cewa hakan baya rasa nasaba da barazanar da shugaban kasar, Amurka Donald Trump ya yi na kai hari Najeriya domin kare Kiristoci da ya ce ana yiwa kisan kare dangi.
A ranar 31 ga watan Nuwamba ne, Trump ya sake saka Najeriya a cikin jerin kasashen da Amurka ke da matukar damuwa akansu kan yadda ake kashe Kiristoci a kasar.
Jim kadan bayan haka ne Trump sakataren ma’aikatar yaki ta Amurka da ya yi shirin ko ta kwana kan yadda za a kai hari Najeriya.

                                    