
Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta yi nasarar cin Fuenlabrada a wasan sada zumunta na farko da kungiyar ta yi don tunkarar kakar da za a fara daga watan Agusta.
Real Madrid ta yi nasara a karawar da ci 3-1 a fafatawar da suka yi a Valdebebas.
Fuenlabrada mai buga karamar gasa ta biyu a Sifaniya ta tsare gida a wasan, amma hakan bai hana Victor Chust da Martin Odegaard da kuma Mariano ci wa Real kwallayen ba.
Sai dai kuma fitattun ‘yan wasn Real Madrid ba su buga fafatawar ba, sakamakon wasu na hutu, wasu kuma na wakiltar kasashensu a gasar kwallon kafa.
Wasan da Real ta yi dama ce ga matasan kungiyar don nuna rawar da za su taka da zarar Carlo Ancelotti ya zabi aiki tare da su, kuma shine ya ja ragamar wasan.
Real Madrid za ta ziyarci Rangers a Scotland, domin buga wani wasan sada zumunta ranar 25 ga watan Yuli.
Real wadda ba ta lashe kofi a kakar da aka kammala ba, za ta fara karawar La Liga ranar 14 ga watan Agusta a gidan Alaves.