Real Madrid vs Barcelona: ‘Yan wasan da za su buga El Clasico

Barcelona ta ziyarci Real Madrid, domin buga wasan mako na 29 a gasar La Liga da za su kara a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.

Kungiyoyin biyu sun hadu sau biyu a bana, inda Real Madrid ta ci 3-2 a Spanish Super Cup a Saudi Arabia ranar 12 ga watan Janairun 2022.

Kafin nan Barcelona ta yi rashin nasara da ci 2-1 a Camp nou a gasar La Liga ranar 24 ga watan Oktoban 2021.

Real Madrid tana mataki na daya da maki 66 a kan teburin La Liga a kakar nan, Barcelona kuwa mai kwantan wasa daya mai maki 51 tana ta uku a teburin.

Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana ‘yan wasan da za su fuskanci Barcelona ranar Lahadi a Santiago Bernabéu.

Benzema ba zai samu damar fuskantar Barcelona wadda itace ta hudu a jerin kungiyoyin idan ya hadu da su sai ya ci kwallo mai 11 a raga, ya kuma bayar da 10 aka ci Barcelona a karawar da ya yi da ita.

Benzema shine kan gaba a cin kwallaye a gasar La Liga ta bana mai 22 kawo yanzu, sai Enes Unal na Getafe da Vinicius Junior na Real Madrid da kowanne keda 14 a raga.

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Diego.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos, Isco, Camavinga.

Masu cin kwallaye: Hazard, Asensio, Jović, Bale, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.

A Barcelona kuwa Dani Alves zai buga wasan El Clasico, wanda ya yi zaman benci a karawa da Galatasaray a Champions League, wanda ba a yi wa rijistar gasar ba.

Sergiño Dest shima bai buga karawar da kungiyar Turkiya ba, sakamakon jinyar rauni.

Tuni Xavi wanda karo na biyu da zai fuskanci Ancelotti ya bayyana ‘yan wasan da suka ziyarci Real Madrid.

Ter Stegen, Piqué, R. Araujo, Sergio, Riqui Puig, O. Dembélé, Dani Alves, Memphis, Adama da kuma Braithwaite.

Sauran sun hada da Neto, Nico, Lenglet, Pedri, L. De Jong, Jordi Alba, Ferran, F. De Jong, O. Mingueza, Eric, Aubameyang, Gavi and Arnau Tenas.

Wadanda ke jinya a Barcelona kawo yanzu sun hada da Dest, Ansu Fati, Sergi Roberto da kuma Samuel Umtiti.

More from this stream

Recomended