‘Rayukanmu Na Fuskantar Barazana’ – Sanatoci Sun Yi Nuna Rashin Amincewa Kan Janye Ƴan Sanda Daga Jikin Manyan Mutane


An samu rsshin jituwa a zauren Majalisar Dattawa ranar Laraba yayin da Sanata Abdul Ningi daga Bauchi ya jagoranci korafe-korafe kan yadda ake aiwatar da umarnin Shugaba Bola Tinubu na janye jami’an ’yan sanda daga Manyan Mutane (VIPs).

Sanatocin sun nemi a ware su daga cikin wadanda za a cire wa ’yan sanda, kamar yadda ake yi wa Shugaba da Mataimakin Shugaba na kasa, Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai da gwamnonin jihohi da mataimakansu. Sun ce ba za su yarda a maida su “kayan zargi” ba.

Shugaba Tinubu ya umarci Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da ya janye jami’an da ke tsaron VIPs saboda matsalolin tsaro da ke ƙaruwa. An umarci bangaren Special Protection Unit da ya mayar da jami’an da ke aiki a gidajen VIPs zuwa ofisoshinsu.

Sanata Ningi ya ce an cire shi daga tsaron ’yan sanda tun da safiyar Laraba duk da cewa wasu VIPs a Najeriya har yanzu suna da ’yan sanda a tare da su. Ya nemi a aiwatar da umarnin “cikin gaskiya daga sama har ƙasa”.

Ningi ya kuma yi zargin cewa wasu ’yan kasuwa, ’ya’yan manyan jami’an gwamnati da ’yan wasa har yanzu suna da ’yan sanda.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya ce shugabancin majalisar ya tattauna batun ranar Talata. Ya bayyana cewa suna kokarin shawo kan fadar Shugaban Kasa domin a cire sanatoci daga jerin VIPs da za a janye musu ’yan sanda.

More from this stream

Recomended