
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Real Madrid ta yi rashin nasara a gidan Rayo Vallecano da ci 1-0 a wasan mako na 35 a gasar cin kofin La Liga da suka fafata a ranar Lahadi.
Rayo wadda take ta biyun karshe wato ta 19 a kasan teburi ta ci kwallon ne ta hannun Adrian Embarba Blazquez a bugun fenariti minti 23 da fara wasa.
Wannan ne karon farko da Rayo ta doke Real Madrid tun bayan shekara 22 a gasar cin kofin La Liga, wato tun 1-0 da ta yi nasara a gida a kan Madrid ranar 19 ga watan Fabrairun 1997.