Rashin musabaha ya sa an ki bai wa Musulmi damar zama ‘yan kasa

[ad_1]

Musabaha

Hakkin mallakar hoto
Science Photo Library

Image caption

Ma’auratan sun ki yin musabaha da mutanen da ba jinsinsu ne ba

Jami’ai a Switzerland sun ce an hana wasu ma’aurata Musulmi izinin zama ‘yan kasar saboda sun ki amincewa su yi musabaha da jinsin da ba nasu ba lokacin da suka je ganawa.

Jami’an sun bayyana daukar wannan mataki ne ranar Juma’a, suna masu cewa ma’auratan sun gaza yin biyayya ga tsarin kasar na daidaiton jinsi.

Ma’auratan, wadanda aka yi wa tambayoyi kan bukatar da suka shigar ta neman zama ‘yan kasar watannin da suka wuce, sun yi ta fama kafin su amsa tambayoyi daga wadanda ba jinsinsu ba ne.

Kwanaki kadan da suka gabata, wata Musulma ‘yar kasar ta Switzerland ta yi nasarar samun diyya bayan da aka hana ta kammala rubuta jarabawar neman aiki saboda ta ki yin musabaha da mutanen da ba jinsinta ne ba.

Hukumomin Switzerland sun ce dole ne duk wanda ke son zama dan kasar ya dace da halaye da zamantakewa irin na ‘yan kasar.

Basu yi karin bayani kan ma’auratan ba – kafofin watsa labaran kasar sun ce sun fito ne daga Arewacin Afirka – sai dai sun ce ma’auratan sun gaza cika sharudan zama ‘yan kasar saboda sun nemi izinin zama ne daga birnin Lausanne.

Magajin birnin Lausanne, Gregoire Junod, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP an bai wa kowa ‘yancin yin addini amma ‘yancin “ba zai wuce na zama dan kasa ba.”

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...