Rasha ta kama Ba’amurke dan leken asiri a Moscow

Rasha na takin saka da kasashen yamma kan zargin leken asiri

Hukumar hana leken asiri ta Rasha FSB ta bayyana cewa ta kama wani Ba’amurke dan leken asiri a Moscow.

Ta ce ta kama mutumin Paul Whelan ne a ranar 28 ga watan Disamba a babban birnin kasar, Moscow, inda aka gurfanar da shi a kan zargin ”leken asirin kasa.”

Hukumar hana leken asirin ba ta yi wani karin bayani a kan batun ba.

Idan har Kotu ta kama shi da laifi, za yai iya kwashe shekara 10 zuwa 20 a gidan kaso, kamar yadda kafar yada labari ta Tass ta ruwaito.

Zargin leken asiri na cikin abubuwan da suka auku tsakanin alakar Rasha da Birtaniya da Amurka.

A farkon wannan watan ne, Amurka ta kama wata ‘yar Rasha Maria Butina da zargin yi wa Rasha aiki, da yin kutse cikin kungiyoyin ‘yan jam’iyyar Conservatives.

Haka zalika a watan Maris, Birtaniya da kasashen yamma sun kori ma’aikatan jakadancin Rasha sama da 100 bayan zargin kokarin kashe tsohon dan leken asirin Rasha Sergei Skripal da diyarsa Yulia a Salisbury.

Rasha ta musanta zargin inda ita ma ta kori ma’aikatan jakadancin kasashen yamma da dama.

More from this stream

Recomended