Ranar Hausa: Wasannin gargajiya a wajen taron da aka gudanar a Rano

Masu sana’o’in gargajiya da masu wasnnin gargajiya musamman na gado sun baje kolinsu inda suka yi wasnnin da suka kayatar da mutane.

Suma makaɗa da mawaƙa maza da mata sun gudanar da wasanni a wajen.

Baya ga wannnan, an kuma saurari bayanai daga masana inda suka nuna muhimmancin ranar ta Hausa.

A shekarar 2015 ne aka fara bikin ranar Hausa ta duniya, don fadakar da masu magana da harshen kan muhimmancin sa.

More from this stream

Recomended