Ranar Bada Agaji Ta Duniya

[ad_1]

Majalisar dinkin duniya (MDD) ce ta ware wannan rana domin tunawa da wadanda tarzoma da rikice-rikice ya ritsa dasu a saasan duniya, wadanda suka hada da ma’aikatan agaji da suka mutu ko suka jikkata.

Ofishin hukumar kula da ayyukan ceto da jin ‘kai ta MDD dake Najeriya ta fitar da wata sanarwa ta musamman dangane da wannan rana.

A shekara ta 2008 ne zauren MDD ya amince da kebe wannan rana, biyo bayan wani harin 19 ga watan Agustan shekarar 2003, akan hedikwatar Majalisar a birnin Baghdaza na kasar Iraqi, wanda ya hallaka mutane 22 da suka hada guda cikin manyan ma’aikatan ofishin a Iraqi Sergio Vieira de Mello.

Tun wancan lokaci ne hukumomi da kungiyoyin bada agaji da ayyukan ceto ke bukukuwan wannan rana, ta hanyar gudanar da gangami da laccocin ilimantar da jama’a game da muhimmancin aikin ceto da kuma kare lafiya da mutunci mutanen da tarzoma ta ritsa dasu kana da jami’an ceto dana jin ‘kai.

Sanarwar da aka fitar na dauke da sa hannun babban jami’in ofishin Mr Edward Kallon, ta ce tun bayan farmakin ‘yan tarzoma a hedikwatar MDD dake Bagadaza a shekara ta 2003, fiye da mutane dubu 4 ne tarzoma ke ritsawa da su a sassan duniya cikin kowacce shekara, inda wasu daga cikin su ke mutuwa da dama ke jikkata kana wasu kuma ake tsare su ko kuma ayi garkuwa da su.

Sanarwar ta ce a kowace shekara, ana samun batutuwa a kalla 300 kan cin zarafin mutanen da rikici ya ritsa dasu a bangarorin duniya, cikin su kuwa har-da ma’aikatan jin ‘kai.

A cewar sanarwar, kimanin mutane miliyan 65 wadanda suka hada mata da yara suka rasa mutsugunnan su a sassan duniya, sanadiyyar rigingimu da tarzomar yaki, kana da kuma ayyukan take hakkin bil’adama.

Yayin da ma’aikatan ceto ke kokarin tallafawa wadanda ke cikin mawuyacin yanayi sanadiyyar farmakin kungiyoyin tarzoma wadanda ke amfani da kananan yara, a hannu guda kuma jami’an jin ‘kan dake kokarin samar da abinci da magunguna na fuskantar barazana.

Mr Edward Kallon a cikin sanarwar ya lura cewa fararen hula na ci gaba da kasancewa cikin kuncin rayuwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, mai fama da rikicin mayakan Boko Haram.

Sanarwar ta ce take hakkin bil’adama da karan tsaye ga dokokin ‘kasa da wadanda ke bada kariya ga mata da yara, na ci gaba da zama ruwan dare a yankin na arewa maso gabas.

Tun daga shekarar 2009 fiye da mutane dubu 26,000 aka kashe a lardin na Borno, inji sanarwar, yayin da aka kona dubban gidaje da kauyuka kuma aka tilastawa dubban iyalai tsarewa daga muhallan su.

A cewar babban jami’in hukumar ayyukan jin ‘kan ta MDD a Najeriya, su-ma ma’aikatan kiwon lafiya dake aikin ceto ba su tsira ba, inda ma’aikatan jin ‘kai uku suka mutu kuma aka sace wasu uku a kauyen Rann na jihar Borno a bana, yayin da wani jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya ya rasa ransa a yankin Damasak cikin makon jiya.

Ya ce MDD tayi tir da batun sace ma’aikatan agajin tare da kira ga bangarorin dake rikici da juna su baiwa ma’aikatan jin ‘kai sukunin kaiwa ga mutanen dake bukatar agaji, kamar yadda dokar ‘kasa da ‘kasa tayi tanadi.

Mr Edward Kallon a cikin sanarwar ya yi kira ga hukumomin Najeriya suyi duk abin daya kamata wajen bada kariya ga mutanen dake zaune a yankin arewa maso gabas, da kuma sauran sassan kasar masu fama da rikici.

Haka kuma ya bukaci sauran masu ruwa da tsaki su hada hannu da hukumar MDD mai kula da ayyukan jin ‘kai, domin kare fararen hulda tare da ma’aikatan agaji daga farmakin ‘yan tarzoma.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

[ad_2]

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...