Kwamitin bincike da Gwamnan Jihar Plateau, Barr. Caleb Manasseh Mutfwang ya kafa domin gano musabbabin hare-haren da ke ci gaba da addabar jihar, ya bayyana cewa aƙalla mutane 12,000 ne aka kashe, yayin da ƙauyuka 450 suka lalace daga shekarar 2001 zuwa 2025.
Kwamitin mai mutum 10, wanda tsohon Janar Nicholas Rogers (Rtd) ya jagoranta, an kafa shi a ranar 20 ga Mayu, 2025. Ya gudanar da bincike a sassa daban-daban na jihar, tare da tattaunawa da al’ummomin da abin ya shafa, hukumomin tsaro da kuma wadanda suka tsira daga hare-haren.
A cewar Janar Rogers, rahoton ya tabbatar da cewa hare-haren da ake zargin ‘yan bindiga Fulani da makiyaya masu dauke da makamai ke yi, sun jawo barna mai girma ga rayuka da dukiyoyi. Ya ce adadin mutanen da aka kashe na iya fiye da abin da aka rubuta, domin akwai wadanda ba a kai rahoton su ba.
Rahoton ya nuna cewar, an lalata kaso 35% na dabbobi, kaso 32.5% na al’ummomi sun rasa matsugunnai, kaso 16.8% an lalata abincinsu, kaso 9.9% an rusa gidaje, sannan kaso 3.4% na filaye aka kwace ba bisa ka’ida ba. Haka kuma, rahoton ya bayyana cewa rikicin ya yi tasiri sosai kan walwalar jama’a, al’adu, da tattalin arzikin jihar.
Yayin da yake mikawa Gwamna Mutfwang rahoton a gidan gwamnati da ke Rayfield, Rogers ya ce: “Wannan tashin hankali an tsara shi ne, akwai wata manufa ta musamman, kuma sakamakon sa abin takaici ne. Amma cikin wannan hali akwai damar jagoranci nagari, haɗin kai da kuma zaman lafiya na gaskiya.”
Da yake mayar da martani, Gwamna Mutfwang ya gode wa kwamitin tare da tabbatar da cewa rahoton zai isa hannun Gwamnatin Tarayya don daukar mataki. Ya ce tuni aka fara ɗaukar ma’aikata zuwa Operation Rainbow domin karfafa tsaro, inda sama da jami’ai 1,000 za a tura horo a mako mai zuwa.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen yakar talauci, gyaran ababen more rayuwa da kuma habaka ilimi. Ya roƙi al’ummar jihar da su rungumi zaman lafiya a matsayin mafita ta gaskiya.
Rahoto: Mutane 12,000 Sun Rasa Rayukansu, An Lalata Ƙauyuka 450 a Plateau Cikin Shekaru 20
