Raheem Sterling ya karbi kambun yaki da wariyar launin fata

Raheem Sterling da Gareth Southgate

Hakkin mallakar hoto
Getty Images


Kocin Ingila Gareth Southgate ne ya mika wa Raheem Sterling kyautar

Dan wasan gaba na Manchester City Raheem Sterling ya bayyana cewa yana so ya zama abin kwatance ga ‘yan wasa masu tasowa jim kadan bayan an ba shi kambun yaki da wariyar launin fata a harkar kwallon kafa a Ingila.

Dan wasan Inglan ya kuma soki gidan jaridu game da yadda suke bayar da rahotanni kan ‘yan wasa bakar fata, ya kuma bukaci a tsaurara hukunci ga magoya baya da ke nuna wariya gare su.

An girmama Sterling ne a harabar gidan talabijin na BT Sport ranar Alhamis.

“Ya kamata ka zama abin kwatance ga masu tasowa,” in ji Sterling mai shekara 24.

“Lokacin da na je Liverpool na tarar da ‘yan wasa kamar Steven Gerrard, wanda ya zama abin koyi a gare ni, kasancewarsa gwarzo a gare ni ya sa nake tunanin zama kamarsa.

“Kana koyar abubuwa ne daya bayan daya sannan kuma ka aikata su a ciki da wajen fili.

“Ina magana ne a kan abin da ya faru da ni, ban yi tsammanin abin zai jawo ce-ce-ku-ce da yawa ba.

“Na yi kokari ne Kawai na jawo hankalin mabiyana a Instagram. Abin ban sha’awa ne yadda mutane suka dauki abin kuma suke kokarin kawo sauyi.”

  • Ko Man City za ta kafa tarihin cin kofuna hudu?
  • ‘Yan wasa 6 da za su iya barin United a karshen kakar bana

Kocin tawagar Ingila Gareth Southgate ne ya gabatar da kyautar ga Sterling, inda ya ce dan wasan ya yi tasiri matuka kan al’ummar Birtaniya”.

“Na yi aiki da Sterling na tsawon shekara biyar. Natsuwarsa da hankalinsa ababen birgewa ne,” in ji kocin.

“Hakan ya taimaka masa kwarai wajen ci gaban wasansa da kuma wajen fili. Abin ya fito fili cikin wata shida da suka gabata, kuma ina ganin ya yi matukar tasiri ga al’ummar Birtaniya.”

Rahotanni sun ruwaito cewa an yi wa Sterling kalaman wariyar launin fata daga magoya bayan Chelsea a wasan da Chelsea din ta doke Man City da 0-2 a watan Disamba.

Hakan ya sa ya wallafa wani bayani a shafinsa na Instagram, inda ya soki gidan jaridu kan yadda suke bayar da rahotanni kan ‘yan wasa bakar fata.

A watan Janairu an ruwaito cewa dan wasan ya rubuta wasika zuwa ga wani karamin yaro magoyin bayan Man City.

A cikin wasikar ya fada wa yaron cewa “ya jajirce sosai kada ya bari a sace masa gwiwa game da burikansa”.

An nuna wa Sterling wariya tare da Danny Rose da kuma Callum Hudson-Odoi a wasan da Ingila ta yi da Montenegro a wasan cancantar shiga gasar cin kofin Turai ta European Championshop a watan Maris.

A farkon watan Afrilu an zabe shi a matsayin “tauraron Birtaniya a fagen wasanni” kuma “abin koyi” bayan an ba shi kyautar British Ethnic Diversity Sports Awards ta 2019.

More from this stream

Recomended